A ranar Laraba 6 ga watan Satumba ne kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa za ta yanke hukunci kan karar da jam’iyyun siyasa biyar suka shigar; PDP, Labour Party (LP), Action Peoples Party (APP), Allied Peoples Movement (APM) da Action Alliance (AA), suna kalubalantar fitowar Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa a zaben ranar 25 ga Fabrairu, 2023.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa zaman Panel na mutane biyar na alkalan yana karkashin jagorancin mai shari’a Justice Haruna Tsammani.
A ranar da za a yanke hukunci, Alkalan biyar za su yi shawara da yuwuwa su kada kuri'a don yanke hukunci na karshe, idan aka samu sabani kan batutuwan da aka gabatar a gaban shari'a. Hukuncin dai ba shi ne na ƙarshe ba, saboda wanda bai ji daɗinsa ba zai iya ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Koli.
Alkalan da ke jagorantar kotun su ne:
1. Justice Haruna Tsammani – Babban magatakardar kotun daukaka kara
2. Justice Stephen Adah – Kotun daukaka kara (Asaba division)
3. Mai shari’a Monsurat Bolaji-Yusuf – Kotun daukaka kara (Asaba Division)
4. Justice Moses Ugo – Kano division
5. Justice Abba Mohammed – Kotun daukaka kara ta Ibadan.
Published by isyaku.com