Da duminsa: An cafke saurayi da ya kashe mahaifinsa ya cire mazakuta da hakorarsa don yin tsafin samun dukiyaJami'an So-Safe Corps, a jihar Ogun sun kaa wani saurayi dan shekara 20 mai suna Ridwan bayan ya kashe mahaifinsa ya cire sassan jikinsa.

$ads={1}
Wata sanarwa daga shugaban rundunar (Dr) Soji Ganzallo ta hannun Kakakin rundunar Moruf Yusuf, ya ce saurayin ya kashe mahaifinsa ranar Alhamis 31 ga watan Agusta da misalin karfe 12 na dare. Ya cite al'aura da hakora hudu daga bakin mahafinsa.

Sai dai saurayin ya tsere bayan aikata laifin kuma daga bisani jami'ai suka kama shi a maboyarsa. Ya gaya wa jami'ai cewa wani Boka mai suna Baba Kekere ne ya bukaci ya kashe mahaifinsa ya kawo wadannan sassa domin yin tsafin samu  dukiya.

$ads={1}
Kakain rundunar ya ce saurayin ya ki gaya masu inda za a sami Baba Kekere. An mika saurayin ga jami'an yan sanda don ci gaba da bincike.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN