Sakataren Din-din-din na Ma'aikatar Filaye da gidaje na jihar Kebbi TPL Abubakar Ahmed, ya kafa kwamiti don duba korafe-korafen mutanen garin Kamba kan zance Filaye da gonaki.
TPL Abubakar tare da manyan jami'an Ma'aikatar Filaye da gidaje na jihar Kebbi ranar Alhamis 24 ga watan Agusta 2023, sun zauna a Ma'aikatar tare da wakilan jama'ar da ke da korafi inda aka tattauna lamurra cikin lumana da fahimtar juna.
Kazalika Sakataren ya ce ya kafa Kwamitin ne don gano gaskiyar abin da ya faru. Kuma wajibi ne yan kwamitin da ya kafa su tantance gaskiyar lamarin domin Ma'aikatar ta yi wa kowa adalci domin samun zaman lafiya da ci gaba mai dorewa.
Kwamitin zai tantance masu Filaye da Gonaki na gaskiya, a zo da rahotu, kada a bar mutum ko daya cikin masu hakki, kada a mance da mutum ko daya, tare da tabbatar da cewa ba a sa siyasa ciki ba. Daga karshe kwamiti zai kawo rahotu.
Kwamitin ya hada da wakilan mutum biyu daga cikin masu gonaki, biyu daga wakilan masu Filaye, jagoran masu korafin, Hakimin yankin, tare da Mataimakin Daraktan Filaye na Ma'aikatar, hafsoshin Ma'aikatar na yankin (Zonal officers) da kuma jami'an tsaro.
Latsa nan ka kalli Hotuna:
Published by isyaku.com