Yan bindiga sun yi wa jami'an Kwastam 2 kisar gilla a jihar Kebbi


Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan ta'adda ne sun kashe jami’an hukumar kwastam biyu na hukumar hana fasa kwabri ta jihar Kebbi.


Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Kwastam ta Najeriya reshen jihar Kebbi Mubarak Mustapha ya fitar dasanarwar.

Kakain hukumar ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Birnin kebbi a ranar Juma’a 25 ga watan Agusta, 2023 wanda shafin labarai na isyaku.com ya samu.


 Sanarwar ta kara da cewa:


 “SANARWA

MUMMUNAR KISAN JAMI'AN kwastam 2 da 'yan bindiga suka yi a JIHAR KEBBI


A ranar Alhamis, 24 ga watan Agusta, 2023, da misalin karfe 0128 na dare, tawagar jami’an rundunar hukumar kwastam ta Najeriya, a yayin da suke gudanar da aikin bincike kan sakamakon sahihan bayanai akan titin Bunza – Dakingari – Koko. Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne suka buda masu wuta da bindiga a cikin wata motar Toyota Corolla mai launin toka.


A rikicin da ya barke, jami’an hukumar guda biyu masu suna Alhaji Kabiru Shehu, Sufeto na Kwastam da Abdullahi Muhammad, mataimakin kwastam na biyu suka mutu.  Tuni dai aka yi jana’izar jami’an kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.


Yayin da ake addu’ar Allah ya jikan marigayin, rundunar Kwastam ta kaddamar da farautar wadanda ake zargin da nufin kama su tare da gurfanar da su gaban kuliya.


Shugaban Hukumar Kwastam na jihar Kebbi, Ben Oramalugo, ya jajanta wa iyalan mamatan kan wannan mummunan lamari da ya faru, ya kuma yi addu’ar Allah ya ba su ikon jure wannan rashi.


 Shugaban rundunar ya kuma bukaci jama’a da su rika bayar da bayanan sa-kai game da motsin da ake zargin masu fasa-kwauri da sauran masu aikata laifuka.  Ya tabbatar wa irin wadannan masu ba da labarin sirrin cewa za a kare sirrinsu".


Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN