Dala FM ta wallafa cewa yanzu haka ke nan da ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa reshen jihar Kano ke ci gaba da gudanar zanga-zangar lumana, wanda za su wuce gidan gwamnatin Kano.
Yanzu haka dai ƴan ƙungiyar da kuma wasu rukunin ƙungiyoyi masu rajin kare haƙƙin bil adama ne harma da ma'aikata suka bayyana domin shiga cikin jerin Zanga-zangar tare da rakiyar jami'an tsaron ƴan sanda, wadda za'a gudanar jahohin ƙasar nan 36.