EFCC ta kama matasa 23 da ake zargi da aikata damfara ta yanar gizo a Sokoto


Jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC sun kama wasu mutane 23 da ake zargi da damfara ta yanar gizo a gidan Bafarawa da ke cikin birnin Sokoto.



 An kai samame a unguwar Bafarawa dake yankin Kalkalawa a jihar Sokoto bayan wani bincike da jami’an leken asiri suka yi tare da sanya ido sosai ya tabbatar da cewa samarin na rayuwa fiye da yadda suke da rayuwa ba tare da samun sahihin hanyar samun kudin shiga ba.



 Wadanda aka kama an bayyana su da Joy Ofem, Azeez .o.  Naimot, Ibrahim Amadu, Aigbekan Daniel, Adedayo Michael, Imran Mubaraq, Oliyide Habeeblah, Wasiu Lukman Adekunle, Musa Abdulaziz, Abdullahi Ibrahim, Adejoh Nebiu Muhammad, Ibrahim Mubarak, Ahmed Ibrahim Abdullahi, Abdullahi Sanusi Adejoh, Umar Idris, Muhammad Nuhu, Faisal Ahmed  , Aliyu Ismail, Elijah Adebayo, Abubakar Bashir, Sakariya Ibrahim, Balogun Abdulayyan as well as Buni Husaini.



 Wasu daga cikin kayayyakin da aka kwato sun hada da kirar Corolla Sport 2009 mai.launi Ja, Farar Corolla 2015, Laptop daban-daban guda 16, Generator 1, wayoyi daban-daban 30, da MTN Routers 2.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN