Yanzu-Yanzu: Babbar Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Tsohon Gwamnan Da Ake Zargi da AlmundahanaBabbar Kotun birnin tarayya Abuja ta yi fatali da ƙarar da hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziki zagon ƙasa (EFCC) ta shigar da tsohon gwamnan Imo, Rochas Okorocha
.

Punch ta ce Alkalin Kotun, mai shari'a Yusuf Halilu ne ya kori ƙarar yayin yanke hukunci kan ƙarar da EFCC ke tuhumar tsohon gwamnan da almundahana da cin mutuncin Ofis. Legit ya wallafa.

Alkalin Kotun ya ce tuhumar da EFCC ke yi wa Sanata Okorocha raina shari'a ne saboda hukumar ta shigar da makamanciyar wannan kara kan wanda ake zargi a babbar Kotun tarayya.

Bisa haka Kotun ta kori ƙarar nan take bisa hujjar cewa babbar kotun tarayya ta riga ta wanke tsohon gwamnan daga zargin da EFCC ta shafa masa a watan Disamba, 2022.

Idan baku manta ba a watan Mayun shekarar da ta gabata, jami'an hukumar EFCC suka mamaye gidan Sanata Okorocha da ke Maitama a babban birnin tarayya Abuja kuma suka kama shi.

Hukumar ta yi zargin cewa Okorocha ya yi fatali da, "Dukkan gayyatar da ta aika masa bayan ya tsallake sharaɗin belin da ta ba shi tun da farko."

Amma a ɓangarensa, Okorocha, wanda ya shiga tseren neman tikitin shugaban ƙasa a inuwar APC, ya zargi EFCC da garkuwa da shi a cikin gidansa ba gaira ba dalili.

Menene asalin zargin da EFCC take wa Okorocha?

A ranar 24 ga watan Janairu, 2022, EFCC ta shigar da tuhume-tuhume 17 da take wa tsohon gwamnan waɗanda suka shafi wawure kuɗin talakawa da kadarori da suka kai biliyan N2.9.

Hukumar na zargin Okorocha da aikata laifukan a tsakanin 2011 zuwa 2019 lokacin da yake kan kujerar gwamnan Imo, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN