Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu na ganawa yanzu haka da shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Adamu, da sakataren jam'iya, Iyiola Omisore a Aso Rock, Abuja.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa jiga-jigan biyu sun dira fadar shugaban ƙasa mintuna kalilan kafin ƙarfe 5:00 na yamma ta cika ranar Laraba, 5 ga watan Yuli.
Daga isarsu, suka wuce kai tsaye zuwa ofishin shugaban kasa suka fara taron a sirrance.
Wannan gana wa na zuwa awanni 24 bayan APC ta nesanta kanta da sunayen jagororin majalisar tarayya da aka sanar ranar Talata, 4 ga watan Yuli 2023.
Idan baku manta ba APC ta ce bata da alaƙa da sabbin jagororin majalisa da aka ji shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, sun sanar a zauren majalisa.
Published by isyaku.com