Ƴan bindiga sun halaka jami'an sojoji mutum bakwai a wani kwanton ɓauna da suka yi musu a jihar Zamfara.
Ƴan bindigan sun farmaki ƙauyen Kangon Garacce a yankin Dangulbi, cikin ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara, ranar Litinin inda suka halaka mutane da dama. Legit Hausa ya wallafa.
Wani mazaumin Dangulbi mai suna, Lawal Dangulbi, ya gayawa Channels tv a ranar Talata cewa sojojin sun je kai ɗauki ne a ƙauyen bayan sun samu kiran gaggawa kan harin da ƴan bindigan suka kai a ƙauyen, lokacin da aka yi musu kwanton ɓauna.
"Ƴan bindigan sun raba kansu ne, wasu suna kai hari a ƙauyen yayin da wasu suka tsaya a wajen ƙauyen domin hana sojoji kai wa mutanen ƙauyen ɗauki, sun yi wa sojojin kwanton ɓauna inda suka halaka bakwai daga cikinsu." A cewarsa.
Ƴan bindigan sun kuma halaka mutane masu yawa a yayin harin
A cewarsa aƙalla mutum 20 mazaunan ƙauyen ƴan bindigan suka halaka a yayin harin, a cewar rahoton Ripples Nigeria.
Duk da dai har yanzu hukumomin sojoji a jihar Zamfara basu ce komai ba dangane da lamarin, wani majiya daga É“angaren sojoji wanda ya san halin da ake ciki dangane da lamarin, ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Ya bayyana cewa jami'an sojoji bakwai aka halaka a mummunan harin na ranar Litinin.
Ƴan bindiga sun daɗe suna kai farmaki a jihar Zamfara inda suka halaka mutane da dama da lalata dukiyoyi, yayin da a wasu lokutan su ke sace mutane domin biyan kuɗin fansa.
Published by isyaku.com