Mota ta kutsa shinge, ta kashe jami'in hukumar kwastam a jihar Kebbi


Kwanturolan yankin Costoms ya jajantawa iyalan jami'in Kwastam Aminu Abdullahi wanda aka kashe bayan mota da ke gabatowa ta kade shi a baking aiki.

 Kakakin hukumar Kwastam PPRO na jihar Kebbi, Mustapha Mubarak a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ya ce lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Alhamis, 13 ga Yuli, 2023 da safe a lokacin da wata mota kirar Toyota Corolla ta kirar shekarar 2015 dauke da chassis mai lamba 2TBURHE3FC456204 ta kutsa cikin shingen jami'an hukumar a, karamar hukumar Yauri ta jihar Kebbi.

An garzaya da jami’in zuwa Babban Asibitin Yauri domin a kula da lafiyarsa, bayan da aka yi mata agajin gaggawa;  An kai shi asibitin kashi na Wammako, a karamar hukumar Wammako a jihar Sakkwato.  Abin takaici, ya rasu da wannan safiya lokacin da yake amsa magani a cikin dare.

Wanda ake zargin mai suna Abdulwasiu Salawudeen da ke tuka motar tuni aka kawo shi hedikwatar rundunar ta Kebbi domin ci gaba da bincike.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN