Wani aradu da ake zargin ‘yan uwan wadanda aka yi garkuwa dasu ne suka shirya ya kashe wasu mutane uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a kauyen Oro Ago da ke karamar hukumar Ifelodun a jihar Kwara.
Vanguard ta tattaro cewa wata majiya daga kungiyar ci gaban Oro-Ago, ODU, kungiyar al’adu ta ’yan asalin yankin, ta tabbatar da faruwar lamarin,
An samu labarin cewa wadanda aka yi garkuwa da su a garin sun baiwa ‘yan banga na yankin kwangila, inda suka sha alwashin cewa za su yi amfani da layukan cikin gida wajen magance masu garkuwa da mutane, wadanda suka addabi garin da kewaye.
A cikin faifan bidiyon lamarin, an gano cewa wadanda tsawar ta rutsa da su, ana zargin wasu gungun masu garkuwa da mutane takwas ne, wadanda rahotanni suka ce suna gudanar da ayyukansu a garin Iwo da ke karamar hukumar Isin ta jihar kimanin makonni biyu da suka gabata.
Hoton bidiyon mai tsawon minti daya da dakika 13, ya nuna gawarwakin wasu matasa uku da ke rubewa, wadanda ake kyautata zaton 'yan shekara 20 ne, sun kone kurmus a wani daji, tare da kudaje a ko'ina.
Da aka tuntubi kwamishinan ‘yan sandan jihar Kwara, Ebunoluwarotimi Adelesi, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce tuni rundunar da jami’anta suka fara bincike kan lamarin.
Shugaban ‘yan sandan ya ce za a tabbatar da sahihancin lamarin bayan bincike mai zurfi.
Published by isyaku.com