Jaridar The Nation ta ruwaito cewa shugaban kasar ya bayyana hakan ne a wata wasika da ya aike wa majalisar da kakakin majalisar Tajudeen Abbas ya karanta yayin zaman majalisar a ranar Talata, 11 ga watan Yuli.
Shugaba Tinubu ya ce kudaden za su bai wa talakawa da marasa galihu ‘yan Najeriya damar shawo kan tsadar biyan bukatun yau da kullum.
Shugaban ya ce hakan zai yi tasiri ga mutane kusan miliyan 60.
Domin tabbatar da sahihancin tsarin, ya ce za a yi musayar dijital kai tsaye zuwa asusun masu cin gajiyar.
Published by isyaku.com