Ana rade-radin cewa yana kokarin satar wayoyin lantarki ne da lalata na’urar taranfoma kafin daga bisani wutar lantarki ta kama shi.
Shugaban makarantar, Mista Chukwujindu Anyikwa, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya shaidawa Vanguard cewa ya kai rahoton faruwar lamarin ga hukumomin da suka dace wadanda suka hada da “Hukumar Kula da Ilimi ta Sakandare (SEMB) a jihar, da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Enugu (Enugu Electricity Distribution Company). EDC) wanda daga baya ya ziyarci wurin da lamarin ya faru."
Kungiyar tsofaffin samarin makarantar ce ta bayar da tallafin taransfoma.