An kama wani mutum da ya kulle matarsa da kuma azabtar da matarsa da yunwa na tsawon shekaru biyu a Borno
‘Yan sanda a jihar Borno sun kama wani mai suna Abdullahi Isa, bisa zarginsa da cin mutunci, kullewa tare da azabtar da matarsa da yunwa kusan shekaru biyu.
Wata mai fafutukar kare hakkin mata da yara, Kwamared Lucy D. Yunana, wanda ta tabbatar da faruwar lamarin ta ce an kama wanda ake zargin ne a unguwar Gwange 3 da ke Maiduguri a ranar Juma’a 30 ga watan Yuni, 2023.
A cewar Madam Yunana, Bulama na Gwange ta kai ma’aikatanta zuwa gidan wanda ake zargin inda matar ta kasance a kulle kusan shekaru biyu.
“Alhamdu lillahi ma’aikatanmu suna gudanar da wani shiri na wayar da kan jama’a kan SGBV a Gwange a lokacin da Bulama na yankin ya kai ma’aikatanmu gidan da aka kulle ta, kuma abin da suka gani ya yi muni, ya sa muka sanar da hukumar da abin ya shafa don ceto rayuwar matar. ”
Ta bayyana cewa sun je wajen ne tare da Kodinetan Hukumar Kare Hakkokin Dan Adam na shiyyar Barr. Jumai Mshelia, kuma ta gan ta a cikin daki, cikin mummunan yanayi da rashin mutuntaka.
Ta kara da cewa an kai ta asibiti inda likitoci ke aikin farfado da ita.
Published by isyaku.com
Subhana lillahi Allah ya kiyaye gaba. Amma me ta yi masa ne haka?
ReplyDeleteKarya kake yi wallahi ba wani aljani ka ci amanar matarka
ReplyDeleteSannu dakokari Malam isiyaku
ReplyDelete