Juyin Mulkin Nijar: Jama'a sun far wa 'yan siyasa akan titi tare da cinna wuta a HQ jam'iyyar PNDS (bidiyo)


Magoya bayan juyin mulkin sojoji a Nijar sun kai hari kan shalkwatar hamɓararren shugaban ƙasar, inda suka cinna wuta tare da jifa da ƙona motocin da ke gaban ginin
. Rahotun BBC Hausa.

Rukunin masu cinna wutar sun ɓalle ne daga cikin wasu ɗumbin mutanen da suka yi dandazo a gaban ginin majalisar dokokin ƙasar don nuna goyon baya ga sojoji masu juyin mulki, inda aka ga wasu na ɗaga tutocin Rasha.

Rundunar sojojin ƙasar a yanzu ta mara baya ga dakarun da suka ƙwace mulki kuma suke tsare da Shugaba Mohamed Bazoum tun ranar Laraba.

Rasha ta bi sahun sauran ƙasashen duniya da Majalisar Ɗinkin Duniya wajen kira a saki Bazoum.

Mai shekara 64, wanda aka zaɓa a matsayin shugaban Nijar shekara biyu da ta wuce, babban abokin ƙawance ne ga Ƙasashen Yamma a yaƙin da suke yi da masu iƙirarin jihadi a Afirka ta Yamma.

Amurka da Faransa, tsohuwar uwargijiyar mulkin mallakar Nijar, duka suna da sansanonin sojoji a ƙasar mai arziƙin yuraniyam kuma sun yi Allah-wadai da juyin mulkin.

Sakataren wajen Amurka Anthony Blinken ya zanta da Bazoum inda ya yi masa alƙawarin "cikakken goyon bayan" gwamnatin Amurka

Shugaban Jamhuriyar Nijar ɗin wanda sojoji suka hamɓarar da gwamnatinsa a ranar Laraba, ya wallafa wani saƙo a shafinsa na tuwita da ke nuna alamun turjiya.

Lamurra sun sauya ne a Nijar bayan da sojoji masu gadin fadar gwamnati suka yi garkuwa da Bazoum.

Ministan harkokin waje na Bazoum ya ce juyin mulkin bai samu goyon bayan sauran sojojin ƙasar ba, to sai dai babban hafsan sojin ƙasar ya sanar da cewa suna goyon bayan masu juyin mulkin.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN