Jerin sunaye sabbin kwamishinonin Yan sanda, Kebbi, jihohi 8


Hukumar kula da harkokin 'Yan sanda (PSC) ta amince da nada tare da tura kwamishinonin 'yan sanda takwas zuwa wasu jihohin kasa.

 PSC ta kuma yabawa Mukaddashin Sufeto Janar na ‘yan sanda (IGP), Kayode Egbetokun, bisa bin ka’idar da ta yi.

 Sai dai hukumar na sa ran IGP a cikin shawarwarin nasa na gaba zai hada da karin jami’an shiyyar Arewa maso Gabas da Kudu maso Gabas har yanzu ba su samu kashi 15 cikin dari ba kamar yadda aka yanke a taronta na karshe.

Sunayen sabbin kwamishinonin yansanda


 A cewar wata sanarwa a ranar Juma’ar da ta gabata ta hannun jami’in hulda da jama’a na PSC, Ikechukwu Ani:

 “Sabbin kwamishinonin ‘yan sandan jihar da aka nada sune;  Godwin Aghaulor yanzu Cp jihar Borno;  Adelesi E. Oluwarotimi, CP jihar kwara;  Adebola Ayinde Hamzat, CP na Jihar Oyo;  Augustina Ogbodo, CP jihar Ebonyi, da Samuel Titus Musa, CP jihar Kebbi.

 “Sauran su ne Aderemi Olufemi Adeoye, CP reshen jihar Anambra;  Stephen Olarewaju, CP jihar Imo, da Alamatu Abiodun Mustapha, CP jihar Ogun”.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN