Rahotanni daga karamar hukumar Jega a jihar Kebbi na cewa ana fargaban wasu budare Tara sun nutse a cikin ruwa sakamakon hadarin kwalekwale.
Majiyarmu ta ce lamarin ya faru me a Mashayar dan kale a mazabar kokani Ward da ke garin Jega, inda mata budare daga garin Unguwar Kurya su tara (9) suka nutse
Majiyar ta ce Sarkin Ruwan Jega karkashin Masarautar Jega sun jagoranci kungiyar Matsunta da masu lalabe domin ceto wayannan bayin Allah,
Ana kyautata zaton an ceto yan mata guda biyu, daya da ranta aka garzaya da ita Asibi. Daya kuma an ceto ta bata da Rai. An hannanta ta ga Yan uwanta,
Yanzu haka anakan neman sauran yan matan guda bakwai a cikin ruwan,
Kokarin mu na jin ta bakin shugaban Karamar hukumar Jega ta wayar salula ya ci tura, domin dai bai amsa kiraye-kiraye da muka yi masa a wayarsa ta salula ba.
Published by isyaku.com