Yayin da Sanata Yari ya kasance sabo a Majalisar Dattawa, tafiyar siyasar sa da nasarorin da ya samu abu ne na a jinjina. Alfijir Hausa ya rahoto.
Kafin ya zama Sanata, Yari ya taba zama Gwamnan Jihar Zamfara na tsawon wa’adi biyu, daga 2011 zuwa 2019.
Kwarewar da ya samu a harkar mulki da shugabanci ta ba shi gogewar da zai rika bibiyar dambarwar siyasar kasa.
Zamansa na gwamna ya samu gagarumar nasara, kuma ya samu karbuwa a bisa kokarinsa na bunkasa jihar Zamfara.
A yayin takarar shugabancin majalisar dattawa, Sanata Yari ya nuna abin a yaba masa, inda ya samu kuri’u 46.
Wannan nasarar na da matukar muhimmanci musamman ganin cewa ita ce karon farko da ya yi takarar neman mukamin.
Yayi matukar nuna iyawarsa na samun goyon baya da yin tasiri ko da a matsayinsa na sabon shiga Majalisar Dattawa.
Bayan tafiyarsa ta siyasa, Yari ya shahara da ayyukan alheri da kuma jajircewarsa a fagen siyasa.
Ahmad Musa Jega
Ya tabbatar da kansa a matsayin mai wayar da kan jama’a a jihar Zamfara, kana yana cudanya da jama’a da fahimtar bukatunsu.
Wannan ba ma kawai ya sa ya samu farin jini a tsakanin al’ummar yankin ba har ma ya kara fito da karbuwar sa a fadin Nijeriya.
Shigar Sanata Abdulaziz Yari a takarar shugabancin majalisar dattawa na nuni da bunkasar sa a fagen siyasar kasa.
A yayin da yake hawa kujerar naki a siyasar Najeriya, ya zo da dimbin gogewa, da tushe, da kuma shahara wajen gudanar da mulki mai inganci.
Kasancewar sa a majalisar dattawa ya yi alkawarin zama mai tasiri da kuzari, wanda zai ba da gudummawa ga ci gaban Najeriya baki daya.
Sanata Abdulaziz Yari, bayan takararsa ta neman shugabancin majalisar dattawa, ya kasance mai rajin tabbatar da ‘yancin ‘yan majalisar, da nufin kaucewa duk wani tunanin ba daidai ba.
Matakin da ya dauka na yin takara da ‘yan majalisar dattawan Kudu da wasu ‘yan siyasa daga shiyyar sa ta Arewa-maso-maso-Yamma ya nuna yadda ya jajirce wajen gudanar da siyasa mai adalci.
Sai dai kuma sakamakon rashin samun nasarar takararsa na neman shugabancin majalisar dattawa ya kawo wasu kalubale a yankin Arewa maso yamma.
Nadin da ake sa ran nadin na shugabannin majalisa daga yankin Arewa maso Yamma bai samu ba, kuma hakan ya nuna cewa rashin zabar Abdulaziz Yari ya bayar da gudunmawa.
Sai dai duk da haka, suna da fatan kan imaninsu na cewa Sanata Yari zai ci gaba da samun nasarori da taka rawar gani a fagen siyasar Najeriya.
Sanata Abdulaziz Yari ya kuma nuna rashin amincewa da bukatar fadar shugaban kasa wanda a yayin da yake son tabbatar da ‘yancin kai na majalisar .
A yayin da Sanata Yari ke ci gaba da tafiyar da harkokinsa na siyasa, kudurinsa na tabbatar da tsarin dimokuradiyya da samar da ‘yan majalisa mai cin gashin kanta ya tsaya cak.
Da yardar Allah, ana sa ran gudummawar da ya bayar a fagen siyasar Nijeriya za ta dore kuma ta bunkasa.
A karshe dai yunkurin Sanata Abdulaziz Yari na neman kujerar shugabancin majalisar dattawa a kan Sanata Godswill Akpabio ya sa shi ya fito fili aka dada sanin sa a sassan Najeriya.
A matsayinsa na tsohon Gwamnan jihar Zamfara da ya yi wa’adi biyu, nasarorin da ya samu da kuma tarihinsa sun bayyana kansu.
Kidayar kuri’un da ya yi da kuma gangamin yakin neman zabe na nuna karuwar karbuwarsa a kasar.
Fitowar Sanata Yari a fagen siyasar kasa wani ci gaba ne mai kayatarwa wanda ke da alƙawarin aiwatar da ayyukansa na gaba da kuma gudummawar da zai bayar a fagen siyasar Nijeriya
Ahmad Musa Jega shugaban al’ummar Jihar Kebbi a Kano ya wallafa.