Daliban Sakandare sun lakada wa Malami dukan tsiya saboda ya hana su satar amsa


Gungun wasu dalibai sun ci zarafin malaminsu mai suna Kolawale Shonuga kan hana daya daga cikinsu satar amsa. Legit ya wallafa.

Daliban su 10 sun ci zarafin malamin ne a ranar Talata 18 ga watan Yuli a makarantar Isanbi Comprehensive a karamar hukumar Ikenne da ke jihar.

Malamin ya sha duka bayan hana daliban satar amsa

Malamin ya kama daya daga cikinsu Ashimi Adebanjo mai shekaru 18 yayin kula da jarabawar a makarantar inda ya kwace tare da yaga takardarsa.

Bayan an tashi a makaranta, daliban sun tare malamin a bakin mashigar makarantar tare da masa duka, Daily Trust ta tattaro.

Daya daga cikin daliban, Kazeem Adelaja ya buga masa sanda a kai yayin da sauran suka ci gaba da dukansa.

'Yan sanda sun cafke daliban
'Yan sandan yanki da ke ofishin Remo sun kawo samame wurin da abin ya faru tare da kama 10 daga cikin daliban, cewar Premium Times.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Omotola Odutola ta ce malamin ya kai rahoton abin da ya faru a ofishin yanki na Remo.

Rahotanni sun tabbatar da tura yaran zuwa kotu don daukar mataki amma mai hulda da jama'a na hukumar 'yan sanda bai yi bayani a kan kama daliban ba.

Gwamnatin jihar ta yi Allah wadai da irin wanna aika-aika inda ta ce ba za ta bari irin wannan rashin tarbiya na faruwa a jihar ba.

Mai ba wa gwamnan jihar shawara akan harkan ilimi, Farfesa Abayemi Arigbabu shi ya bayyana haka a birnin Abeokuta

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN