Da duminsa: Farashin litar man fetur ya kara tashi a Najeriya, ya haura N600 a gidan man NNPCL


Rahoton Daily Trust da safiyar Talata, ya tabbatar da cewa farashin litar man fetur a Najeriya ya ƙara tashi zuwa N617 a tsakiyar birnin tarayya Abuja.

Yayin wata ziyara da wakilin jaridar ya kai gidan mai mallakin kamfanin mai na ƙasa (NNPCL) da ke Abuja ya tabbatar da cewa farashin ya tashi daga N539 zuwa N617 kan kowace lita. Legit ya wallafa.

Wani kwastoma na daban wanda ya ƙara tabbatar da wannan ci gaban ga wakilin jaridar Daily Trust, ya shaida cewa, "Tabbas da gaske ne, yanzu na sayi mai kan N617 kowace lita."

Meyasa aka samu ƙari kan farashin a NNPCL?

A halin yanzu ba bu wanda ya san dalilin tashin farashi litar mai ba zato ba tsammani kuma mahukunta ba su ce komai dangane da lamarin ba har kawo yanzu.

Sai dai ana hasashen cewa tsadar man ba zai rasa nasaba da hasashen da 'yan kasuwar mai suka yi a kwanakin baya cewa Litar mai ka iya kai wa N700 nan gaba.

Hukumar kula da harkokin Man Fetur ta Najeriya (NDMPRA) ba ta ce komai ba kan sakon da jaridar ta aike mata don tabbatarwa har zuwa yanzu da muke haɗa muku rahoto.

Wani mazaunin Abuja, James Arpashe ya shaida wa jaridar Premium Times cewa, "Yanzu na sayi mai kan N617 a kowace lita a yankin cibiyar kasuwanci."

A jihar Ogun kuma farashin litar mai ya tashi zuwa N568 a gidajen man kamfanin NNPCL yayin da masu motoci ke ta fafutukar samun mai.

Meya jawo haka?

Mai magana da yawun kamfanin mai na ƙasa, Garba Deen Muhammad, ya bayyana cewa kamfanin zai yi ƙarin haske kan lamarin nan ba da jima wa ba.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN