Da Dumi-Dumi: Sanatan APC Na Shirin Murabus Daga Majalisar Dattawa, Sahihan Bayanai Sun Fito


David Umahi, mataimakin shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa ta 10, ya fara shirye-shiryen sauka daga muƙaminsa na Sanata, jaridar Bussinesday ta rahoto. Legit ya wallafa.

Umahi, tsohon gwamnan jihar Ebonyi ya fara yunkurin sauka daga matsayin sanata ne sakamakon naɗin da aka masa na Minista karkashin mulkin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

Tsohon gwamnan, wanda ke wakiltar mazaɓar Sanatan Ebonyi ta kudu a majalisar tarayya ta 10, yana daga cikin manyan jiga-jigan jam'iyyar APC mai mulki.

Yana cikin manyan jiga-jigan siyasa da shugaba Tinubu ya zaƙulo ya naɗa a a matsayin ministocinsa, waɗanda tuni sunayensu suka isa majalisar dattawa.

Daga cikin waɗan nan jiga-jigan har da abokin Umahi kuma tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyeson Wike, da tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai, Leadership ta rahoto.

A ɗazu shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya tabbatar da zuwan sunayen kuma ya karanto su ɗaya bayan ɗaya a a zauran majalisa ranar Alhamis.

Ya kuma bayyana cewa nan ba da jima wa ba shugaban kasa zai sake turo ƙarin sunayen waɗanda ya naɗa ministoci domin tantancewa.

Tun da jima wa 'yan Najeriya suka ƙosa su ji sunayen ministocin shugabam ƙasa domin sa ido su ga rawar da tawagar zata taka a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN