Majalisar wakilai ta amince da bukatar Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na neman gyara kwarya-kwartar kasafin kudin 2022, jaridar Punch ta rahoto.
Majalisar ta amince da hakan ne bayan bukatar da Tinubu na gabatar na daukar naira biliyan 500 domin tallafawa yan Najeriya da nufi rage radadin janye tallafin man Fetur. Legit ya wallafa.
Gyaran ya tsallake karatu na farko, na biyu da na uku a yayin zaman majalisa a ranar Laraba, 12 ga watan Yuli.
Sai dai kuma, majalisar ta amince da bukatar shugaban kasar a ranar Alhamis, 13 ga watan Yuli bayan mambobin majalisar sun bayar da gudunmawa.
Published by isyaku.com