An kori manyan 'yan sanda 3 masu muƙami, an rage wa wasu matsayi, duba dalili


Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta kasa (PSC) ta amince da korar wasu manyan jami’an ‘yan sanda uku bisa wasu manyan laifuka rashin ɗa'a suka aikata. Legit ya wallafa.

Leadership ta tattaro cewa hukumar ta kuma amince da rage wa wasu 'yan sanda biyar mukamai bayan gano suna wasa a gudanar da ayyukansu.

Mai magana da yawun hukumar PSC, Ikechukwu Ani, ne ya bayyana haka yayin da ya yake ƙarin haske kan abinda aka tattauna a taron hukumar karo na 21.

Taron wanda ya gudana ƙarƙashin jagorancin shugaban PSC, Dakta Solomon Arase, ya ƙarkare ranar Alhamis, 20 ga watan Yuli, 2023.

Waɗanne manyan jami'ai hukumar ta kora daga aiki?

Jami’an ‘yan sandan da hukumar PSC ta kora dai sun hada da mataimakan Sufuritandan ‘yan sanda (DSP) biyu da kuma mataimakin Sufeton ‘yan sanda (ASP).

Babban Sufuritandan na ’yan sanda (CSP) guda ɗaya, Sufuritanda (SP), Mataimakin Sufuritanda (DSP) ɗaya da mataimakan Sufuritandan ‘yan sanda (ASP) guda biyu an rage musu mukami saboda rashin da’a.

PSC ta hukunta jami'ai 14 da tsawatarwa mai tsanani, ta tsawarta wasu yan sanda 6, kana wasu Bakwai kuma sun samu wasiƙun gargaɗi, kamar yadda Vanguard ta tattaro.

PSC ta dawo da wasu jami'ai da aka kora a baya

Hukumar ta kuma maido da wasu jami’ai shida da aka kora daga aiki bayan hukuncin kotu ya ba su gaskiya ko kuma an sake duba kararrakinsu.

A ranar Laraba 18 ga watan Yuli ne dai hukumar ta amince da nadin mataimakin sufeto-janar na ‘yan sanda biyu, Mathew Akinyosola da Slyverster Abiodun Alabi.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN