Yan bindiga sun sake sace Dan kasuwa inyamiri a yankin Ningi

Yan bindiga sun sake sace Dan kasuwa inyamiri a yankin Ningi

Daga Muazu Hardawa Bauchi

Ningi Bauchi state

Rahoton da muke samu yanzu wasu yan bindiga sun kai hari garin Gamji dake karamar hukumar Ningi cikin Jihar Bauchi, inda suka yi garkuwa da wani dan Kasuwa Dan kabilar Igbo mai suna Daniel.

Dan Jarida Muazu Hardawa Bauchi, ya ruwaito cewa Yan bindigar sun shiga garin da misalin karfe 8:40 na daren ranar juma'a, inda sukayi ta harba bindiga daga bisani kuma suka sace Daniel dan Kabilar Igbo wanda yake kasuwanci a garin na Gamji.

Lamarin garkuwa da mutane dai sai sake ƙamari yake yi kuma gwamnati tayi kokari amma har yanzu lamarin na sake daukan sabon salon da ya jefa mazauna yankunan karkara cikin damuwa.

Ko a wannan satin yan bindigar sun sace wani mutum a garin mai suna Yahaya, dan kimanin shekaru 45 a duniya inda suka bukaci a basu Naira miliyan goma a matsayin kudin fansa, amma har yanzu ana musayar bayanai ba a kai ga daidaitawa ba.

Haka kuma a kwanakin baya an sace wani Sarki a garin Tabla da ke Ningi, sai da suka biya naira milyan biyar aka sake shi. 

Ya zuwa wannan lokaci, akwai daidaikun mutane da ke hannun Yan bindiga, amma har yanzu babu labarin su.

Dukkan kokarin da muka yi don jin ta bakin Yan sandan Jihar Bauchi ya ci tura.

By/Daga -  isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN