Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da hakimin garin Balma da ke karamar hukumar Ningi a jihar Bauchi, Alhaji Hussaini Saleh Balma tare da kashe wani dan kasuwa, Alhaji Haruna Dan Osi.
An tattaro cewa masu garkuwa da mutanen sun mamaye kauyen ne a daren ranar Asabar, 10 ga watan Yuni, 2023, inda suka harbe dan kasuwar kafin su tafi da Hakimin kauyen zuwa inda ba a sani ba.
An garzaya da Alhaji Haruna Dan Osi asibitin gwamnatin tarayya dake Birnin Kudu a jihar Jigawa, inda aka tabbatar da rasuwarsa.
BY isyaku.com