Hukumar kashe gobara ta jihar Kwara ta gano gawar wata mata mai suna Misis Jamiu Sikirat mai shekaru 57 a rijiya da ke Ilorin.
Sikirat dake unguwar Ile-Agunko dake unguwar Adeta dake garin Ilorin a karamar hukumar Ilorin ta yamma, ta je diban ruwa a harabar Ile-Onikoko dake unguwar Adeta a lokacin da ta fada cikin rijiya a yammacin ranar Litinin 19 ga watan Yuni 2023 da misalin karfe 6:42 na yamma. .
Kakakin hukumar Hassan Hakeem Adekunle, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar, ya ce an sanar da rundunar ne ta wayar tarho da wani Malam Muhammad Jamiu da ke zaune a unguwar ya yi.
“Duk da haka, ‘yan kwana-kwana sun samu nasarar dauko gawar daga cikin rijiyar, inda daga bisani suka mika gawar ga wani Alfa Abdulganiyu Akuko, dan gidan marigayiyar, a gaban jami’an ‘yan sandan Najeriya, Adewole Division Ilorin,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.
“A cewar rahoton, matar da ta je diban ruwa a rijiyar, kuma a lokacin da take diban ruwan, sai kafarta ta zame daga kasa, a karshe ta fada cikin rijiyar.
By/Daga - Click/Latsa isyaku.com