Tsohon Gwamnan Zamfara, Alhaji Bello Matawalle, ya bayar da gudunmuwar Naira miliyan 200 ga al'ummar jihar daban-daban domin bikin Eid-el-Kabir.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban jam’iyyar APC na jihar, Alhaji Tukur Danfulani, wanda sakataren yada labaran jihar, Malam Yusuf Idris ya fitar a Gusau ranar Asabar.
Danfulani wanda shi ne Shugaban kwamitin rabon kayayyakin ya bayyana cewa wadanda suka amfana sun hada da ‘ya’yan jam’iyyar da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da mata da kungiyoyin matasa da kuma kungiyoyi.
“Sauran wadanda suka ci gajiyar tallafin sun hada da marayu da marasa galihu, malaman addinin Musulunci, masu aikin yada labarai, da masu gudanar da shafukan sada zumunta da dai sauransu.
“Karimcin na da nufin taimaka wa mutane su yi bikin Eid-el-Kabir mai zuwa na 2023 cikin sauki.
“Tuni kwamitin ya fara rabon kudaden ga duk wadanda suka amfana,” in ji Idris Danfulani.
Danfulani, wanda ya godewa Matawalle bisa wannan karimcin ya bayyana hakan a matsayin wanda ya dace da shi domin zai kawo karshen tabarbarewar tattalin arziki a tsakanin ‘yan jihar musamman a matakin kasa.
By/Daga - Click/Latsa isyaku.com