PRESS RELEASE
Hajiya Nafisa Nasir Idris matar Gwamnan jihar Kebbii |
Mai girma matar Gwamnan jihar Kebbi Hajiya Nafisa Nasir Idris (Kauran Gwandu) ta cika alkawarin da tayi ma yan gudun hijira dake garin Ambursa na kai musu sabon generator domin rage musu wahalhalun samun ruwan sha da kuma na sauran abubuwa.
A jawabin shugabansu wanda aka hannunta ma Generator din, ya nuna sun dade suna wahalar neman ruwa inda watarana basu ko samun ruwan gaba daya. Yayi ma Her Excellency, Hajiya Nafisa Nasir Idris (Kauran Gwandu) addu'ar cewa Allah ya saka mata da alkhairinsa da irin ayyukan da take yi musu na alkhairi.
Ya kara da cewa basu san da irin kalaman da zasu yi amfani suyi mata godiya ba sai dai su cigaba da yi mata fatan alkhairi da fatar nasara a mulkinsu.
Muna rokon Allah ya saka mata da mafificin alkhairinsa ya saka mata ladar ayyukan jinkai da take yi a mizani.
Signed;
Ibrahim Mahe
By/Daga - Click/Latsa isyaku.com