Gwamnatin Kano za ta cigaba da rushe-rushe bayan rade-radin tilasta dakatarwa


Gwamnatin jihar Kano ta ja-kunnen al’umma a yunkurin da ta ke cigaba da yi na ganin an dawo da tsarin taswira da ta ke zargin an saba.

Rahoto ya zo daga gidan rediyon Freedom cewa Abba Kabir Yusuf ya bukaci duk wadanda su ke da kaya a inda za a rusa, su dauke dukiyoyinsu. Legit Hausa ya wallafa.

Mai girma Abba Kabir Yusuf ya gargadi wadanda suke gini a filayen al’umma kamar makabartu da wuraren ibada da su gaggauta tattara kayansu.

Sauran wuraren da sanarwar ta yi magana a kai sun hada da asibitoci, jikin ganuwa, filayen ma’aikatu da wuraren shakatawa da wuraren wasanni.

Gwamnatin Abba Yusuf ta ce masu kaya a shaguna ko wasu gine-gine a wadannan wurare da asali gwamnati ta mallaka, su kaucewa yin biyu-babu.

A dauke kaya da gaggawa

Kamar yadda rahoton ya nuna sanarwar ta ce a dauke kayan ne ba tare da bata lokaci ba, amma ba a fadi takamaimen ranar da za a rusa gine-ginen ba.

Legit.ng Hausa ta fahimci Sakataren gwamnatin jihar Kano, Dr. Abdullahi Baffa Bichi ya fitar da sanarwar a madadin gwamna a yammacin Alhamis.

Kafin nan wata majiya ta nuna gwamnatin Kano za ta cigaba da ruguza gidaje, shaguna da sauran gine-ginen da ake zargin an yi su ba a ka’ida ba.

Mutane sun ci ganima

Ganin mutane su na kukan asara duk lokacin da aka yi rushe-rushen musamman cikin dare, shiyasa wannan karo aka ja-kunnen al’umma tun wuri.

Idan hukuma ta rusa wadannan gini cikin dare, zuwa safiya sai a ji bata-gari sun shiga wuraren su na satar kayan jama’a da sunan an samu ganima.

A jiyan ne mu ka ji sabon Gwamnan ya ziyarci makarantar mata da ke Mariri, sannan ya duba lafiyar motocin da za a rika kai yara zuwa karatu.

An kai karar Gwamnati a kotu

A farkon makon nan an ji labari kamfanin Lamash Property Limited ya bukaci Gwamnatin Abba ta biya sa N10bn domin rage zafin rusa Daula otel.

Shi kuma dan kasuwar nan, Alhaji ‘Dan Asabe Abubakar ya ce an jawo masa asarar Naira biliyan 1.4 a sakamakon rusa filin sukuwa da aka yi cikin dare.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN