Da duminsa: An kashe wani mahauci da duka a Sokoto kan zargin batanci ga Annabi


A safiyar yau 25 ga watan Yuni ne wani mutum mai matsakaicin shekaru mai suna Usman Buda ya sha dukan tsiya har lahira, bisa zarginsa da yin kalaman batanci ga Annabi Muhammad.

 Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Ahmad Rufa’i, ya ce da misalin karfe 9:20 na safiyar yau, ‘yan sanda sun samu kiran wayar tarho cewa marigayin wanda mahauci ne, wasu mabiya addinin Musulunci ne suka yi wa mamacin mumunar duka tare da haifar da raunukan ajali.

 ''Bayan samun labarin, kwamishinan 'yan sanda, Kwamandan yankin Metro da  DPO kwanni sun jagoranci tawagar 'yan sanda da dukkan sauran kwamandojin aiki zuwa wurin.  Da isar mutanen sai suka tsere daga inda lamarin ya faru sannan suka bar wanda abin ya shafa a sume inda aka ceto shi aka kai shi Asibitin Koyarwa na Usmanu Danfodio Sokoto (UDUTH) domin yi masa magani daga baya kuma aka tabbatar da rasuwarsa a asibitin da aka ce’’.

 Rufa'i ya ce an samu kwanciyar hankali a yankin.  Ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Ali Hayatu Kaigama psc, ya roki jama’a da su ci gaba da gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, kuma kada su firgita saboda halin da ake ciki.

 ‘’A halin da ake ciki kuma, ana ci gaba da bincike don kamo wadanda suka aikata laifin tare da gurfanar da su a gaban kotu.’’ inji shi.

By/Daga - Click/Latsa isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN