Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandire (JAMB) ta fitar da sabon mafi karancin maki (Cut of mark) na shiga manyan makarantu a zangon 2022/2023.
Daily Trust ta rahoto cewa JAMB ta amince da maki 140 zuwa sama a matsayin mafi karancin makin neman gurbin shiga jami'o'in Najeriya a zangon karatu 2022/2023. Legit ya wallafa.
Shugaban JAMB na ƙasa, Farfesa Is-haq Oloyede, ne ya faɗi haka yayin da yake jawabi kan neman gurbin shiga makarantun gaba da Sakandire a wurin taron tsare-tsaren 2023 a Abuja ranar Asabar.
Farfesa Oloyede ya ƙara da cewa hukumar ta kuma amince da maki 100 a matsayin mafi ƙarancin makin neman gurbin shiga kwalejojin fasaha (Poly) da kwalejojin ilimi (FCE) a faɗin ƙasar nan.
Ya yi bayanin cewa wannan makin da JAMB ta kayyade shi ne mafi ƙaranci, kuma ba tilas bane makarantu su bi, su na ikon ƙarawa ya wuce haka amma kar ya gaza wannan.
By/Daga - Click/Latsa isyaku.com