Marigayin dai mai suna Charles an gano gawarshi shi ne a wani daji dake karamar hukumar Oguta kwanakin baya. PM News ta rahoto.
An yi garkuwa da Charles, sufeton ‘yan sanda makonnin da suka gabata tare da direbar motar da suke ciki a unguwar Ohaji/Egbema.
An tattaro cewa suna cikin mota kirar Hilux ne kuma wasu da suka sace motar suka tare su suka tafi da su inda ba a sani ba.
An ce daga baya an gano gawar direban bayan ya mutu, yayin da Charles ba a san inda yake ba har sai da aka tsinci gawarsa a wani yanayi na rubewa.
Wata majiyar kauye ta ce "an gano gawar Charles a cikin wani daji kwanaki da suka gabata".
Wasu daga cikin abokan aikinsa sun ji zafin kisan da aka yi wa Sufeton ‘yan sanda wanda ya fito daga karamar hukumar Mbaise.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Imo, Henry Okoye, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce rundunar ta fara gudanar da bincike domin cafke wadanda suka kashe shi.
BY isyaku.com