Wani mutum da har yanzu ba a bayyana sunan sa ba, wanda aka ce ma’aikacin BEDC ne, wutar lantarki ta kama shi a lokacin da yake gudanar da gyare-gyare a wata igiyar wayar wuta da ke kusa da jami’ar Benin da ke Ekehuan.
Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, 11 ga watan Mayu, 2023, yayin da mamacin ke bakin aikisa.
A cikin wani faifan bidiyo da aka gani a yanar gizo, an ga mutumin da ke sanye da kayan kariya mai rubutu, BEDC, yana ratsawa daga sandar wutar lantarki.
Shedun gani da ido sun shaida wa jaridar PUNCH cewa mutumin yana tsaye ne a kan sandar kuma kafin su kashe wutar lantarkin ya kama shi.
"Mutumin yana kokarin gyara daya daga cikin wayoyi da ke fadowa lokacin da wutar lantarki ta kama shi," in ji wani ganau.
“Ba na jin an kashe wutar daga na’urar kashe wutar lantarkin na tsakiya kafin ya fara gudanar da gyaran, yana cikin aiki lokacin da aka dawo da wutar lantarki ya kama shi.
“Ya kasance a wurin na kusan mintuna 20 kafin mutane su fara lura da abin da ke faruwa da shi. Amma an makara.”
BY ISYAKU.COM
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI