Mulki: Kwankwaso, Wike da Wasu Yan Adawa 4 da Ka Iya Shiga a Dama Dasu a Mulkin Tinubu


A ranar 29 ga watan Mayu ne za a rantsar da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu bayan kammala wa’adin shugaba Muhammadu Buhari da ya fara mulki a 2015. Legit Hausa ya wallafa.

Gabannin rantsar da shi, zababben shugaban kasa Tinubu ya kulla alaka da wasu jiga-jigan ‘yan siyasa da suka hada da ‘yan jam’iyyun adawa.

Bayan sanar da shi a matsayin zababben shugaban kasa a zaben da aka gudanar a watan Faburairu, Tinubu a ya sha kiran a yi hadaka don kafa gwamnatin gamayya da za ta kawo ci gaba ga kasa.

A kasa, jerin sunayen ‘yan jam’iyyun adawa ne da ake tsammanin Tinubu zai yi aiki da su a gwamnatinsa.

Rabiu Kwankwaso

Kwankwaso babban dan siyasa ne kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP a zaben da ya gabata, yana daya daga cikin wadanda ake sa ran za su iya shiga gwamnatin Tinubu a dama dasu.

Kwankwaso a kwanan nan ya tabbatar da haduwarsu da Tinubu a kasar Faransa yayin da ya bayyana zagewarsa don yin aiki da sabuwar gwamnatin.

Nyesom Wike

Yana daya daga cikin manyan ‘yan jam’iyyar adawa ta PDP wanda ake tsammanin zai yi aiki da Tinubu a sabuwar gwamnati da za a kafa a 29 ga watan Mayu.

A lokacin zaben shugaban kasa da aka gudanar, Wike ya yi iyakar bakin kokarinsa don ganin Tinubu da APC sun ci jihar Rivers, kuma ya cika burinsa na ganin ya salwantar da goben jam’iyyar PDP a jihar.

Ayo Fayose

Tsohon gwamnan jihar Ekiti kuma jigo a jam’iyyar PDP yana daya daga cikin wadanda ba sa maganganun batanci ga Tinubu.

Ana sa ran Tinubu zai iya aiki da shi a sabuwar gwamnatin da za a kafa a wannan wata, ganin yadda jiga-jigan jam’iyyar PDP suka juyawa dan takararsu Atiku Abubakar baya.

Chimaroke Nnamami Nnamani
Tsohon gwamnan jihar Enugu ne kuma Sanata har na tsawon wa’adi biyu a majalisar dattawa da ya wakilci Enugu ta Gabas.

A lokacin zaben shugaban kasa da aka gudanar, Nnamani ya fito fili ya goyi bayan Tinubu wanda hakan ya yi sanadin korarsa a jam’iyyar ta PDP.

Daga baya ya yi takarar sanata in da ya rasa kujerar ga dan takarar jam’iyyar Labour.

Reno Omokri

Tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara kuma jigo a yakin neman zaben Atiku, a baya-bayan nan ya yabi halayen zababben shugaban kasa Tinubu.

A martanin da ya yi wa Peter Obi kan maganarsa da yace mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya fi cancanta akan Tinubu, Omokri ya ce Tinubu ya fi Obi da Osinbajo cancanta sau goma.

Lamidi Apapa

Shugaban zagin jam’iyyar Labour a kwanan nan an zargi cewa Bola Tinubu da jam’iyyar APC suke daukar nauyinsa don kawo cikas a karar da aka shigar akan korafe-korafen zabe.

Duk da cewa Apapa ya musanta zargin da ake masa na cewa ana daukar nauyinsa, amma ya tabbatar cewa idan Tinubu ya gayyace shi zai amsa gayyatar.

Ya bayyana hakan ne ta bakin lauyansa a zaman da aka yi yau a gaban kotun raba gardamar zabe da aka zauna.

A baya, Atiku ya ce bai amince Tinubu ya yi nasara a zaben bana ba, don haka a tabbatar da ba a rantsar dashi ba

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN