Sanata Aliyu Wamakko ya kayar da mataimakin gwamnan jihar Sokoto Manir Muhammad Dan'iya ya ci gaba da zama a majalisar dattawa. Daily trust ta ruwaito.
Wamakko ya samu kuri'u 141,468 yayin da Dan'iya ya samu 118445 bayan kammala zaben da aka gudanar a ranar Asabar din da ta gabata don tantance wanda ya lashe zaben Sanatan Sokoto da Arewa.
Kafin a ce zaben bai kammalu ba, Wamakko ne ke kan gaba da Dan’iya da kuri’u sama da 10,000.
Wamakko wanda ya taba zama gwamnan jihar a wa’adi biyu kuma shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya kasance a majalisar dattawa tun shekarar 2015.
Ana dakon sakamakon sauran shiyyar Sanata biyu.
BY ISYAKU.COM
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI