Kayya: An caka wa matashi wuka har Lahira lokacin da yake rabon fada tsakanin abokinsa da wani mutum


An caka wa wani magidanci mai shekaru 39 mai suna Sunday Orishagbemi wuka har lahira a lokacin da yake kokarin sasanta rikici tsakanin wasu mutane biyu a Zango Daji Quarters a karamar hukumar Adavi ta jihar Kogi.

 An tattaro cewa lamarin ya faru ne a ranar Juma’a 21 ga watan Afrilu, lokacin da wani abokin marigayin a mahadar Ganaja, Lokoja, ya je yin fitsari kusa da wani gini mallakin daya daga cikin mazauna unguwar.

 A cewar wani ganau, mai ginin ya bijire wa lamarin inda aka fara cece-kuce a tsakaninsu.

 Marigayin ya damu da faruwar lamarin, ya shigo domin sasanta rikicin da ke tsakanin abokinsa da mutumin.

 Ana cikin haka ne aka ce dan mai gidan ya fito da wuka ya daba wa Orishagbemi har lahira.

 Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, SP William Ovye Ayah, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a wata hira da manema labarai a Lokoja a ranar Asabar, 22 ga watan Afrilu, ya ce an kashe marigayin ne a Park Okada da ke Zango Daji, inda ya ce rundunar ta kama wanda ake zargin.

 PPRO ya bada tabbacin cewa wanda ake zargin za a gurfanar da shi a gaban Kotu da zarar an kammala bincike kan lamarin.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN