Daga Karshe Tinubu Ya Bayyana Zabin Sa a Shugabancin Majalisar Dattawa


Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya shirya tsaf domin haÉ—a tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Sanata Godswill Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattawa da Sanata Barau Jibrin a matsayin mataimakin sa, rahoton Daily Trust ya tabbatar.

Akpabio da Barau suna daga cikin Æ´an takara 9 da ke neman shugabancin majalisar dattawa ta 10, wacce ake sa ran za a rantsar da ita a ranar 13 ga watan Yuni.

Majiyoyi masu tushe sun tabbatarwa da Daily Trust cewa, zaɓaɓɓen shugaban ƙasar, ya gayawa Akpabio da Barau wannan hukuncin na sa da ya yanke a yayin wani taro a birnin tarayya Abuja.

Tsohon gwamnan na jihar Legas, ya sanya labule a ranar Talata da Akpabio, Barau, Sanata Opeyemi Bamidele da gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji

Majiyoyi sun tabbatar da cewa a lokacin ganawar ta su, wacce Tinubu ne ya sanya aka gudanar, an buƙaci Barau da ya janye takarar sa domin samun daidaito, adalci da raba daidai ta fannin addini.

Wani ɗan majalisa daga Kudancin Najeriya, ya ce an shawo kan Barau ya janye takarar sa ne domin daidaituwa da zaman lafiya a ƙasa.

A kalamansa:

"An ce masa ya haƙura da takara domin a samu kirista a matsayin shugaban majalisar dattawa ta 10."

"Bayan an gama roƙon sa ne zaɓaɓɓen shugaban ƙasa ya gayawa Barau cewa yana son ya yi aiki da Akpabio a matsayin mataimakin shugaban majalisar dattawa."

Da ya ke ƙara tabbatar da hakan, wani mamba a kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na jam'iyyar APC, ya bayyana cewa Tinubu ya tuntuɓi Akpabio da Barau, akan shawarar da ya yanke na su shugabanci majalisar dattawan.

"Bana wajen lokacin da aka yi taron, amma mutum biyu da suka halarci taron sun gaya min hukuncin da Asiwaju ya yanke. Gaskiya ne ya zaɓi Akpabio da Barau a matsayin shugaba da mataimaki." A cewarsa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN