Yan mata sun bayyana wa Aminiya abubuwa daban-daban da ke birge su, har su ji suna son namiji. Jaridar Aminiya ta ruwaito.
Waddannan abubuwan in ji matan, suna cikin wadanda suke fara kalla har su kai ga jan hankalinsu su amince su fara soyayya da namiji.
Sai dai kamar yadda kowa ke da dabi’u da halayen da suka bambanta shi da wani, to haka yake a gurin ’yan mata ma, kowace akwai abin da take kula da shi a gurin namiji, da zai sa ta so shi.
Aminiya ta tattauna da wasu mata kan abin da namiji zai yi ya burge su har su yi soyaya da shi.
Wata budurwa mai suna Nusaiba, ta bayyana wa Aminiya cewa, “Ni yadda namiji ke tafiya ne abin da ya fi burge ni da shi.”
Ita kuwa wata mai suna Nafisa Bello cewa ta yi, “Yanayin kwalliya da tsarin namiji da kuma yanayin hankalinsa ne suka fi burge ni. Idan namiji na tunani kamar yaro karami duk kwalliyar shi, zan iya barin shi.”
Sai dai ita kuwa wata budurwar mai suna Goodness Auta, ta ce, “Nauyin aljuhun namiji ne zai sa ni son shi, da kuma tsayi da kyawun shi.”
Ga karin wasu abubuwan da matan suka ce sun fi burge su da maza:
Tsawo
Kyan fuska
Kwalliya da sa kaya
Natsuwa
Kyau
Launin fata
Diri/Kira
Hankali
Yanayin kamshin turare
Kafa
A karshe, ‘yan mata da dama sun bayyana cewa kyau namiji suke kula da a farko.
BY ISYAKU.COM
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI