Tsohon mataimakin gwamnan jihar Ekiti da ya sauka, Bisi Egbeyemi, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 78 a duniya. Legit ya wallafa.
Jaridar Punch ta tattaro cewa Mista Egbeyemi ya rike kujerar mataimakin gwamna a lokacin mulkin gwamna Kayode Fayemi. Ya yi aiki a tsakanin 2018 zuwa 2022.
Bayanai sun nuna cewa tsohon mataimakin gwamnan ya rasu ne da kusan misalin karfe 8:00 na daren ranar Jumu'a bayan fama da yar gajeruwar rashin lafiya.
Bugu da ƙari, an tattro cewa Marigayin ya cika ne a wani Asbitin kuɗi da ke Ado-Ekiti, babban birnin jihar Ekiti.
BY ISYAKU.COM
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI