Za mu yi maganinka: Dattijon Arewa ya fusata da kalaman El-Rufai da yace babu dattawa Arewa

 


Arewacin Najeriya - Martani ya biyon bayan kalaman gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai da ke cewa babu sauran dattawa a Arewacin Najeriya, Punch ta ruwaito. 


Legit.ng ya wallafa cewa martanin na fitowa ne daga bakin tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiju Bafarawa, wanda ya bayyana rashin jin dadinsa da sakin layin El-Rufai.


A cewar Barafarwa, ya kamata El-Rufai ya san kalaman da yake furtawa, domin irin wadannan sun yi kama da cin fuska da yin jam’i wajen kakaba rashin dattaku ga dukkan dattawa a Arewa.


Bafarawa ya yiwa El-Rufai martani mai zafi


Da yake zantawa da kafar labarai ta BBC Hausa, Malam Nasir El-Rufai ya tono batutuwa da ke alaka da yiwa dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Tinubu zagon kasa, kuma yace daga dattawan Arewa ne.


A tattaunawar, an ji El-Rufai na cewa shima dattijo ne, domin shekarunsa 63 kuma baya tsoron wani dattijon Arewa da zai nuna masa yatsa.


Ba shekaru bane dattako, inji Bafarawa

Shi kuwa da yake martani ga kalaman El-Rufai, Bafarawa cewa ya yi ai ba shekaru bane dattako, ana samun mai kananan shekarun da ya san ya kamata.


A cewarsa, dattako na nufin tunani da sanin ya kamata irin na manyan mutane, wanda ana samunsa a yaro ko babba mai shekaru 100, rahoton BBC.


A cewar Bafarawa


"Sannan da ya ke magana cewa shekarun sa 63, kuma baya ganin da sauran dattijai a arewa, to mu muna ganin waÉ—annan maganganu akwai rashin dattijantaka a cikinsu."

Za mu nuna maka da sauran dattawa a Arewa

A cewar tsohon gwamnan, El-Rufai ne wanda ba dattijo ba, domin a cewarsa hakan ya nuna karara a cikin kalamansa.


Daga karshe bafarawa ya sanar da El-Rufai cewa, Arewa ba sa’ar mutum guda bane, ta fi karfin mutum daya, domin duk wanda ya ja da ita ba zai gama lafiya ba.


Kuma yace dattawan Arewa za su koya masa hankali da sanin ya kamata, kuma za su ba duk wani irinsa kunya a zabe mai zuwa ta hanyar nuna masa akwai sauran dattawa a Arewa.


Kadan daga batutuwan da El-Rufai ya tabo sun hada da na sauya fasalin kudi da kuma wa'adin da CBN ya sanya na tattara tsoffi.

1 Comments

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

  1. abdulkarim zubairuSaturday, February 04, 2023

    Wannan yayi daidai,agwada mass,baisan abundayakeba,

    ReplyDelete
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN