Wani mutum da har yanzu ba a tantance ba, ana zargin ya ya yanke jikiya fadi ya mutu a wani banki da ke Agbor a jihar Delta bayan ya jira sa’o’i da dama don ya cire kudi.
Lamarin ya faru ne a cikin dakin ajiyar banki da yammacin ranar Alhamis, 2 ga Fabrairu, 2023.
Jaridar Ika Weekly da wasu shaidun gani da ido sun tabbatar da faruwar lamarin a shafin Facebook.
Wani Omole Mike, ya raba hoton marigayin kuma ya rubuta; "Yanzu haka, da misalin karfe 1:30 na rana. Wani ya fadi ya mutu a bankin First Bank of Nigeria, Agbor Branch. Rana: 02-02-2023. Allah Ya Jikansa da Rahma". Ya rubuta.