Kwankwaso: Babu wani dan Najeriya mai hankali da zai zabi APC ko PDP a 2023

 


Dan takarar shugabancin kasa a inuwar jam'iyyar NNPP, Rabi'u Kwankwaso, ya ce babu wani dan Najeriya da ya san ciwon kan shi da zai zabi daya daga cikin APC ko PDP a zaben shugaban kasa na 25 ga Fabrairu. Legit.ng ya wallafa.


Kwankwaso ya bayyana haka ne ranar Litinin lokacin da ya ke jawabi ga magoya bayan sa a wajen taron yakin neman zaben dan takarar gwamna da ya gudana a karamar hukumar Tarauni da ke Jihar Kano.


Rabiu Kwankwaso

Babu Wani Dan Najeriya Mai Tunani Da Zai Zabi APC Ko PDP, In Ji Kwankwaso. Hoto: @MobilePunch Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar


Tsohon gwamnan Jihar Kano Kwankwaso ya bayyana jam'iyyun biyu a matsayin makiyan mata da matasa da sauran yan Najeriya, jaridar The Punch ta rahoto.


Da ya ke jan kunnen magoya bayansa kan su guji tada tarzoma, ya ce jam'iyyar ba zata lamunci kowanne irin magudi ba a zabe mai zuwa.


Ya ce:


''PDP da APC sun mutu kuma duk wanda ya san me yake masa ciwo ba zai goyi bayan su ko ya sake zabar su ba.

''Su ne silar jefa Najeriya halin da ta ke ciki yanzu kuma makiya ne ga mata, matasa da sauran yan Najeriya. Saboda haka dole mu kada su.

''Ku zama masu son zaman lafiya kada a same ku da tada tarzoma, amma baza a maimaita mana abin da ya faru a zaben da ya gabata ba, don haka duk wanda ya kada mana kuri'a zai zama jami'in sanya ido, kayi zabe ka kuma tabbatar an kirga kuri'ar ka."

Ya kuma roki mazauna jihar da kuma yan Najeriya gaba daya da kada su kuskura su siyar da kuri'a.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN