Kididdigar Masu siyayya (CPI) wacce ke gwada sauyin farashin kayayyaki ta bayyana cewa kaya sun yi tashin gwauron zabi da kashi 21.82 a watan Janairun 2023 daga kashi 21.34 a watan Disamba. Legit Hausa ya wallafa.
Bayanin tashin farashin kayayyakin da CPI ta fitar an dake shi ne a ranar Laraba ta karkashin Hukumar Kididdiga ta kasa, NBS.
The Cable ta rahoto cewa, tashin farashin kayayyakin ya nuna karuwar kashi 0.47 idan aka hada shi da na watan Disamban 2022.
Sai dai, idan aka alakanta shi da na shekara-shekara, an samu karin kashi 6.22 kan na watan Janairun 2022 wanda ya kai kashi 15.60.
Karin bayani na tafe…