Babbar magana: An fille kan Sarki yayin rikicin rabon kudi a jihar Delta


Rundunar yan sandan jihar Delta ta ce an halaka basaraken garin Asamokwu, Obi Okwudiki Odumodu. Legit.ng ya wallafa
.


An datse kansa yayin rikicin da ya biyo bayan fada da aka yi kan rabon kudin kason albarkatun man fetur.


Kakakin yan sandan jihar Delta, DSP Bright Edafe ya bayyana hakan a ranar Juma'a a Asaba, rahoton The Punch.


An datse kan Obi Odumodu a ranar Alhamis yayin rikicin da aka yi tsakanin garuruwa biyu a karamar hukumar Ndokwu ta Gabas na jihar Delta.


Punch Metro, a baya ta rahoto cewa wasu bata gari sun kashe basaraken kuma sun kashe sojoji hudu yayin wani hari da suka kai musu inda uku suka mutu nan take daya kuma ya karasa a asibiti.


Amma a wani sabon cigaba, kakakin yan sandan jihar ya ce:


"Rikici ne a tsakanin garuruwa. Sun jayayya ne kan kudi da suka fito daga kamfanonin man fetur da ke aiki a yankin.


"An kashe basaraken a lokacin da ake jayayya tsakanin garinsa da garin da ke makwabtaka kan raba kudin da kamfanin man fetur ta basu.


"Garuruwan suna rikici ne kan ribar kudin man fetur din. Bangarorin biyu suna rikici. Don haka, rikici ne tsakanin garuruwa."


Edefe, ya ce ana kokarin tabbatar da zaman lafiya a garuruwan, ya kara da cewa an kama wadanda ake zargi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN