Yan sandan Sokoto sun fara wani muhimmin aiki kan harkar tsaro ana yanayin yakin neman zabe


Rundunar ‘yan sanda a jihar Sokoto a ranar Litinin din nan ta ce za ta kara kaimi wajen yaki da miyagun laifuka, ciki har da fara ayyukan bazata da binciken ababen hawa a jihar.


Rahotun Kamfanin dillacin labarai na Najeriya NAN ya ce wannan ci gaban na kunshe ne a cikin wata sanarwa da DSP Sanusi Abubakar, kakakin rundunar ya raba wa manema labarai.


Abubakar ya ce an yi sanarwar ne domin wayar da kan jama’a musamman shugabannin jam’iyyar siyasa da ’yan takara da kuma matasan jihar da ke ci gaba da tururuwa.


“Kwamishanan ‘yan sanda, CP Muhammad Gumel, tare da hadin guiwar dukkan mambobin kwamitin tuntuba tsakanin hukumomin tsaro kan harkokin zabe (ICCES) a jihar za su kara kaimi wajen yaki da miyagun laifuka.


"Wannan ya hada da fara aikin Tsayawa na bazata da bincike don kama duk mutumin da aka samu dauke da kowane irin haramtattun makamai a lokacin yakin neman zabe a dukkan sassan jihar," in ji shi.


A cewar PPRO, matakin ya samo asali ne yayin da ake kara zafafa gangamin yakin neman zabe na jam’iyyun siyasa daban-daban.


“Shawarar daukar tsauraran matakan ya biyo bayan nazari sosai kan ayyukan yakin neman zabe da kuma keta ayyukan zabe inda aka ga magoya bayan ‘yan siyasa suna rike da makami wanda ya sabawa dokar da ta dace.


“Saboda haka, bisa wannan sanarwar, ana sanar da jama’a cewa daga yanzu za a gudanar da cikakken bincike a dukkan hanyoyin da aka gano da kuma wuraren fita a jihar.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN