Yadda maigida ya kama matashi mai shekara 24 yana lalata da matarsa mai juna biyu a dakin jinya a gadon asibiti

Yadda maigida ya kama matashi mai shekara 24 yana lalata da matarsa mai juna biyu a dakin jinya a gadon asibiti


Asirin wata mata mai juna biyu ya tonu bayan mijinta ya kamata turmi-tabarya tare da wani mutum dan shekara 24 yana lalata da ita a gadon dakin asibiti inda aka kwantar da ita don jinyar zazzabin ciwon Malariya a gundumar Apac da ke kasar Uganda. Shafin isyaku.com ya samo.

An kamata ne lokacin da mijin matar, Mista Alex Okuta, ya je duba ta bayan ta shafe kwanaki biyar a asibiti kuma ya kama su.

Mista David Wills Ndaula, kwamandan ‘yan sanda na gundumar Apac, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Alhamis, 12 ga watan Janairu, 2023, ya ce an tuhumi wanda aka kama da laifin tada hankalin jama’a.

Ndaula ya shaidawa Daily Monitor cewa ‘yan sanda sun fara bincike kan lamarin.

Mista Joseph Onuk, mai kula da asibitin Apac, ya yi nadamar lamarin da ya yi imanin cewa tun da farko za a iya kauce masa.

"Na dora laifi ga mijin wannan matar" ya kara da cewa, "Ta yaya za ka tura matarka asibiti ka dauki tsawon lokaci ba tare da ka duba ta ba, wasu mazan kullum sai su ce sun shagaltu, idan aka sami wani da ya ke kula da ita zai iya kwace matarka."  Yace.

Mijin matar, mazaunin kauyen Abwal “A” da ke yankin Chegere a gundumar Apac, ya tabbatar da cewa matarsa ​​da ba ta da lafiya ta yi masa magudi.

“Na kai ziyarar bazata asibiti domin duba matata sai na tarar da mutumin nan a kwance tare da matata mai ciki,” ya bayyana cewa an kwantar da matarsa ​​saboda tana fama da zazzabin cizon sauro.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN