Masoyi ya yi wa masoyiyarsa yar shekara 22 dukan tsiya har lahara, duba yadda ta faru


Wani mutum mai suna Mista Arepamowei Koru, wanda ya fito daga yankin Ogobiri a karamar hukumar Sagbama a Bayelsa, ya yi wa budurwarsa mai suna Miss Toma Angolo ‘yar shekara 22 dukan tsiya har lahira. Shafin isyaku.com ya samo.

An ce masoyan biyu suna zaune ne a unguwar mutumin, kafin wannan mummunan lamari ya faru a ranar Talata.

Mazauna unguwar sun bayyana cewa abokanan biyu sun zauna tare ba tare da an samu sabani ba, kafin karamin rashin jituwar da suka yi a ranar Talata ya kai ga fada.

A cewarsu, mai yiwuwa mutumin ya buge ta da karfi, wanda hakan ya sa ta zubar da jini har ta mutu.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya samu labarin cewa kanwar marigayiyar ta rike mai laifin kafin ta sanar da ‘yan sanda da ke yankin Amassoma, inda suka kama shi.

Mahaifin marigayiyar, Mista ServeGod Angolo, ya garzaya da ita asibitin gwamnatin tarayya da ke Yenagoa, amma sai ta mutu kafin su isa asibiti.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an kama wanda ake zargin tare da tsare shi a hukumar binciken manyan laifuka ta kasa (SCID). 

Daga  isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN