Askarawan sojin Najeriya sun kashe shugaban 'yan bindiga, Kachalla Gudau a Katsina


Kasa da kwanaki hudu bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba 'yan Najeriya tabbacin mulkinsa zai tabbatar da samar da tsaro, dakarun rundunar sojin Najeriya sun bindige 'yan bindiga da dama, har da Ibrahim Kachalla Gudau.

Gudau, wani gawurtaccen 'dan ta'adda sannan daya daga cikin shugabannin 'yan ta'adda masu hatsarin gaske, ya na jagorantar tawagar hatsabiban da ke garkuwa gami da halaka mutane a yankunan Kaduna, Katsina, Zamfara da yankin jamhuriyar Nijar, jaridar Vanguard ta rahoto.

An yi imani, tawagar Gudau ta halaka jami'an tsaro bakwai na tsaron farar hula (NSCDC), wadanda 'yan bindiga sukawa kwantan bauna gami da halakasu a jihar Kaduna yayin da suke kan aiki a makon da ya gaba.

Kamar yadda binciken sirrin da aka samu ya bayyana, Gudau, wanda hoton gawarsa yayi yawo a yanar gizo, ya na daya daga cikin wadanda dakarun suka sheke yayin da suka dakile wani gagarumin hari a kauyen Kankami na jihar Kaduna.

Kamfanin dillacin labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito yadda Buhari a makon da ya gabata yayi alkawari ga 'yan kasa kan tabbatar da tsaro gami da mayar da hankali wajen bunkasa tattalin arziki, kafin mika mulki da ranar 29 ga watan Mayu.

Shugaban kasar ya fadi hakan ne yayin da ya tarbi taron mambobin cocin Katolika na Najeriya (CBCN) a gidan gwamnati da ke Abuja, ranar Laraba.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN