An nada mace a matsayin Limamin farko a wani gurin ibada a Najeriya


Cocin Methodist ta Najeriya, ta nada Right Reverend Nkechi Nwosu a matsayin limamin cocin na farko a Najeriya.

Archbishop na Kaduna, Rabaran Joseph Nnonah a ranar Lahadi, 22 ga watan Janairu ya nada Nwosu a matsayin Bishop na Jos a Cocin Christ Methodist Cathedral Church da ke Jos.

Hidimar cocin ta zo ne bayan yanke shawarar taron shekara-shekara na Cocin Methodist a Najeriya da aka yi a shekarar 2022 inda aka zabi Nwosu a matsayin Bishop na Jos.

A nata jawabin, Nwosu ta ce Allah ya sa kowa ya daidaita.  Ta kuma ja hankalin ‘yan Nijeriya da su rika neman fuskar Allah a koda yaushe.

“Dole ne mu fita wurin kuma mu yarda da Allah, mu saurari ruhun Allah, kuma mu yi abin da Allah ya ce mu yi,” in ji sabon bishop.

"Ku yi haka domin Allah ya yi amfani da mu da duk wanda ya dora a kan kujerar don dawo da Najeriya wurin alfahari a Afirka da duniya."

Previous Post Next Post

Information

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN