Yan ta’adda sun kashe mutum 55,430 a Najeriya —Rahoto


Wani rahoto na musamman ya nuna ’yan ta’adda sun kashe akalla mutum 55,430 a sassan Najeriya daga hawan Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari a 2015 zuwa yanzu. Jaridar Aminiya ta ruwaito.

Hakan na nufin a kowace rana ’yan ta’adda na kashe kimanin mutun 20 — a kwana 2,743 da gwamnati mai ci ta ya yi a kan mulki zuwa yanzu — a sassan kasar da ke fama da matsalolin tsaro.

Matsalolin tsaro Najeriya ke fama da su sun da ta’addancin Boko Haram da tun daga shekarar 2009 da hare-haren ’yan bindiga da rikicin manoma da makiyaya da kuma ta’addancin kungiyar IPOB mai neman ballewa daga kasar da kuma rikice-rikicen siyasa.

Rahoton ya nuna daga hawan gwamnatin Buhari a 2015 zuwa yanzu, ’yan ta’adda da sauran masu aikata manyan laifuka a sun kashe mutum 55,430 a sassa daban-daban na Najeriya.

Wani rahoto da cibiyar Tony Blai ta fitar ta bayyana cewa daga 1999 da aka dawo kan tafarkin dimokuradiyya a Najeriya, an kashe akalla mutum 1,525 a sakamakon rikice-rikicen siyasa a kasar.

Cibiyar Tony Blair ta bayyana cewa alkaluman kashe-kashe da aka samu a shekaru 25 da suka gabata  abin damuwa ne lura da karatowar babban zaben 2023 a kasar.

Rahoton na zuwa ne mako biyu bayan Shugaban ’Yan Sandan Najeriya, Usman Baba, ya ce a cikin kwana 50 an samu tashe-tashen hankula 52, yana mai gargadi cewa idan ba a dauki mataki ba, hakan zai iya kawo tasgaro ga zaben 2023.

Rahoton da kafar Daily Trust ta samu ya nuna rikicin zaben 2011 ne mafi muni, inda tarzoma da aka yi na kwana uku, ya yi ajajlin mutum 800, wasu 65,000 kuma suka rasa muhallansu. 

Na biye da shi shi ne zaben 2003, inda mutum 300 suka rasa rayukansu, na uku shi ne zaben 2019 da aka kashe mutum 145, sannan aka yi asarar rayuka 100 a zaben 2015.

A 2003 an rasa mutum 100 bayan a zaben 1999 mutum 80 sun rasa rayukansu sakamakon rikice-rikice siyasa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN